Isa ga babban shafi
Najeriya - Kasuwanci

Kungiyar masu Albasa ta dakatar da safara zuwa kudu maso gabashin Najeriya

Kungiyar masu noman albasa da hada-hadar kasuwancinta ta Najeriya ta dakatar da safarar Albasar zuwa yankin kudu maso gabashin kasar saboda matsalar tsaron da ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB suka haddasa.

Albasa.
Albasa. © CC0 Pixabay/Contributeur
Talla

Yayin sanar da matakin a ranar Laraba, shugaban kungiyar masu Albasar na kasa Aliyu Isa, ya ce sun yanke shawarar ce, bayan da ‘yan bindigar IPOB suka kwace manyan motocinsu na dakon albasa biyu makon jiya a jihar Imo.

Cikin makon nan kungiyar dattawan arewacin Najeriya ACF ta shawarci al’ummar yankin da su kauracewa tafiye-tafiye zuwa yankin kudu maso gabashin kasar, sakamakon barazanar hare-haren ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar  ta IPOB mai neman kafa kasar Biafra.

A watannin baya bayan nan dai hare-haren ‘ya’yan kungiyar IPOB sun karu a sassan yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda suka rika kai farmaki kan gine-ginen gwamnati har da ofisohin ‘yan sanda tare da kashe jami’an tsaron fiye da 120.

A watan Mayu hukumar zaben Najeriya INEC ta wallafa rahoton ake bayyana kaiwa ofisohinta 41 hare-hare cikin shekaru 2, kuma 18 daga cikin ofisoshin da aka aiwa farmakin na jihar Imo, inda ‘yan ta’adda suka kashe Ahmed Gulak, tsohon mai baiwa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan harokin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.