Isa ga babban shafi

Najeriya: An kama wani manomi da ya sanya guba a rijiyoyi guda 9

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya dake Jihar Yobe ta kama wani manomi da ake kira Mohammed Mohammed da ake zargi da sanya guba a wasu rijiyoyi guda 9 dake kauyen Kasesa a karamar hukumar Damaturu.

Gwamnan jihar Yobe Maimala Buni
Gwamnan jihar Yobe Maimala Buni RFI hausa/Abba
Talla

Kakakin Yan Sandan Jihar Abdulkarim Dungus yace a ranar 25 ga watan Mayu ne wanda ake zargin ya sanya maganin kwari a rijiyoyin guda 9 da mutane suke amfani da su wajen shan ruwa da kuma biyan bukatun su na yau da kullum.

Binciken kimiya da aka gudanar daga samfurin ruwan da aka diba a dakunan gwajin kimiya ya tabbatar da gurbata ruwan rijiyoyin da sinadarin ‘fecal coliforms’ wanda ke iya haifar da cutar kwalara da zazzabin typhoeid da wasu nau’oin cutar dake da nasaba da ruwan sha.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar tace wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumar sa akai, amma yace yayi haka ne domin hana makiyaya mamaye gonar sa.

Kakakin Yan Sandan jihar yace jami’an su na kuma kokarin kama makiyayan da manomin ke zargin sun mamaye gonar sa domin gudanar da bincike kan zargin da yake musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.