Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane 88 a kauyuka 8 na Kebbi

A Najeriya ‘yan sanda a Birnin Kebbi sun tabbatar da cewa mutane 88 ne ‘yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Danko-Wasagu  ta jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar a ranar Alhamis.

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin
Talla

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito kakakin   rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar yana cewa kisan ya auku ne a cikin daren Alhamis zuwa Juma’ar nan.

A cewarsa, ko da yake ‘yan sanda na aikin tantance adadin wadanda suka mutu, tuni rundunar ta aike da jami’anta yankin.

Ya ce kashe kashen sun auko ne a kauyukan in Koro, kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iguenge a kaaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbin.

Idan ba a manta ba, a watan Afrilun wannan shekarar ne  ‘yan bindigar suka kashe jami’an ‘yan sanda 9 a karamar hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.