Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Sama da mutane 200 aka kashe a Najeriya a makon jiya

Mutane 201 ne suka gamu da ajalinsu a hannun ‘yan bindiga a cikin mako guda da ya gabata, yayin da wasu 137 suka fada hannun masu satar mutane suna garkuwa da su don neman kudaden fansa.

'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS. AP - Sunday Alamba
Talla

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a shafin yanar gizo a Najeriya, ta ce ta  tattaro alkaluman ne daga jaridu da suka karas da kuma dangi da ‘yan uwan mutanen da aka kashe ko kuma aka yi  garkuwa da wani nasu.

Cikin mutanen da suka gamu da ajalinsu, akwai Ahmed Gulak wanda aka kashe a garin Owerri.

Baya ga wannan, duk dai a makon ne wasu ‘yan bindiga suka kutsa kai wani yanki a jihar Ebonyi suka kashe mutane 30.

A Larabar da ta gabata kamar yadda kakakin sojan Nigeria Brigadier Mohammed Yerima ke cewa, sojoji sun yi  nasarar kama wasu masu safarar bindigogi ta kasa, a yankunan Sokoto zuwa Janhuriyar Nijar, kuma nan take sun yi katarin kamawa da kashe 3.

A cewar Jaridar, jihar Osun ma, ba ta tsira ba domin wasu ‘yan bindiga sun kai kazamin hari bankuna biyu da yammacin Laraba, inda aka kashe mutane 7 ciki har da jamian ‘yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.