Isa ga babban shafi
Najeriya - Boko Haram

ISWAP da Boko Haram sun sake hadewa bayan zaben sabon shugaba

Bangarorin da ke rikici da juna na tsagin mayakan Boko Haram masu biyayya ga Abubakar Shekau da kuma na ISWAP sun dinke barakar dake tsakaninsu tare da zabar sabon shugaba.

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP
Talla

Matakin na zuwa ne makwanni bayan mutuwar Shekau da ya kashe kansa a lokacin mayakan ISWAP suka yi masa kofar rago bayan murkushe mayakansa a fafatawar da suka yi.

Bangarorin na Boko Haram da ISWAP sun sanar da dinke barakar dake tsakaninsu ce a cikin wani hoton bidiyo mai tsawon mintuna 13 da aka nada cikin harsunan Larabci, Hausa da Fulatanci gami da Ingilishi, inda suka bayyana wani Abba Ibrahim Al Khuraishi a matsayin sabon jagoransu.

Cikin bidiyon, wani daga cikin mayakan ya tabbatar da cewa jami’an wasu hukumomi sun taka rawa wajen haddasa rikici tsakaninsu, ko da yake bai bayyana wadanne hukumomi ne ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.