Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Ya zama dole ayi dokar amfani da kafofin sada zumunta - Gbajabiamila

Shugaban Majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila yace ya zama dole a samar da dokokin da zasu takaita wuce gona da iri da ake samu wajen amfani da kafofin sada zumunta wadanda ke yin illa a cikin kasa.

Shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila
Shugaban Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila © Concise News
Talla

Gbajabiamila yace Majalisar dokoki ta dade tana nazari akan daukar matakan da suka dace wajen samar da irin wadannan dokokin da zasu kare jama’a daga illolin wadannan kafofi amma sai ta dinga jan kafa saboda korafin da jama’ar kasar keyi dangane da fargabar hana jama’a bayyana ra’ayoyin su ko kuma fadin albarkacin bakin su.

Shugaban Majalisar wanda ya amince da ci gaban da kafofin suka samar, ya kuma bayyana cewar sun zama wata kafa na haifar da illa daga wasu masu amfani da su ta hanyar da bata kamata ba.

Wasu daga cikin kafofin sada zumunta
Wasu daga cikin kafofin sada zumunta © CC0 Pixabay/LoboStudioHamburg

Gbajabiamila yace kasashen duniya da dama yanzu haka na daukar irin wadannan matakai na sanya dokokin da zasu tabbatar da ingancin wadannan kafofin sada zumunta da kuma wadanda zasu bada damar ladabtar da wadanda suka saba ka’ida.

Dan majalisar yace hakkin su ne su kare ko wane dan Najeriya kuma hakan za su yi wajen gabatar da dokokin da zasu taimakawa jama’a baki daya.

Yunkurin daukar irin wannan mataki na samar da dokokin da zasu kare masu amfani da wadannan kafofi da kuma hukunta wadanda suka wuce gona-da-iri ya gamu da suka a majalisar da ta gabaci wannan.

Matsalolin da aka samu lokacin zanga zangar adawa da cin zarafin Yan Sanda da kuma rikicin gwamnatin Najeriya da kamfanin twitter ya sake bada damar gabatar da sabon yunkuri daga Majalisar na yunkurowa domin gabatar da dokar da ta dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.