Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SIYASA

Tinubu yayi maraba da sauya shekar Gwamnan Zamfara

Jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Jam’iyyar su a matsayin wadda aka kafa ta akan hanyar dimokiradiya abinda ya sa yanzu haka Yan adawa ke rige rigen komawa cikin ta cikin su harda gwamnonin jam’iyyun adawa.

Jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu
Jagoran Jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu REUTERS
Talla

Sanarwar da Tinubu ya rabawa manema labarai sakamakon sauya shekar da Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle yayi tare da wasu Yan Majalisun Jihar yace sauya shekar ta nuna cewar Matawalle ya sadaukar da kan sa wajen samar da shugabanci na gari a jihar sa.

Tsohon gwamnan na Jihar Lagos yace a madadin sa da daukacin ‘yayan Jam’iyyar APC su na maraba da Matawalle wanda ya zama cikakken dan jam’iyya da zai taka rawa wajen ci gaban ta da kuma jihar sa da Najeriya baki daya.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jagoran APC Bola Ahmed Tinubu Nigeria Presidency/Handout via Reuters

Tinubu ya bukaci Matawalle ya hada kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin shawo kan matsalr tsaron da ta addabi jihar Zamfara, yayin da yake cewa kofa a bude take ga duk wani ‘dan adawar dake bukatar ganin ci gaban dimokiradiya a Najeriya.

Kafin sauya shekar Gwamnan Zamfara Gwamnonin Jihohin Ebonyi da Cross Rivers wato David Umahi da Ben Ayade sun fice daga Jam’iyyar su ta PDP zuwa APC.

Tuni Jam’iyyar PDP ta hannun Sakataren ta na Kasa Sanata Umar Ibrahim Tsauri yace zasu je kotu domin kalubalantar sauya shekar da kuma bukatar kotu ta basu kujerar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.