Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Yan bindiga sun kashe makiyaya 7 a Jihar Plateau

Rundunar Yan Sandan Najeriya dake Jihar Plateau tace wasu Yan bindiga sun kashe Fulani makiyaya guda 7 a kauyen Chol dake karamar hukumar Jos ta Kudu.

Hoton dake nuna alamar 'yan bindiga.
Hoton dake nuna alamar 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Kakakin Yan Sandan Jihar ASP Ubah Gabriel wanda ya tabbatar da kisan yace lamarin ya auku ne yammacin jiya alhamis lokacin da 'Yan bindigar suka harbe shanu sama da 40.

Jami’in yace Cibiyar Yan Sandan dake Jihar Plateau ta samu labarin kai harin da Yan bindigar suka yi a kauyen Chol dake Yankin Vwang a karamar hukumar Jos ta Kudu inda aka kashe mutane 6 da shanu 5, kuma nan da nan runduna ta 6 na dakarun dake aikin samar da zaman lafiya ta STF ta tura jami’an ta.

Gabriel yace suna cigaba gudanar da bincike domin gano wadanda suka kashe makiyayan da dabbobin su a Jihar da ake yawan samun tashin hankali tsakanin makiyaya da manoma.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito daya daga cikin mahaifan yaran da aka kashe Abdullahi Jibrin na bayyana cewar wata motar J5 ta kawo Yan bindigar da suka budewa makiyayan wuta kamar yadda daya daga cikin wadanda suka tsira ya shaida musu.

Jibrin yace Yan bindigar sun gudu daga Yankin bayan harin ba tare da kama koda guda daga cikin su ba.

Shugaban hadaddiyar kungiyar Fulanin Najeriya Abdulkarim Bayero da jami’an soji da Yan Sanda dake aiki a karkashin rundunar STF ta 6 na dakarun samar da zaman lafiya na daga cikin wadanda suka halarci Babban Masallachin Bukur inda aka yiwa makiyayan jana’iza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.