Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Yan Sanda sun harbe wata matashiya a Lagos

Yan Sanda Najeriya sun harbe wata matashiya a birnin Lagos lokacin da suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga zangar goyan bayan kafa kasar Yarbawa zalla a Unguwar Ojota.

Sunday Igboho, daya daga cikin masu fafutukar kafa kafa kasar Yarbawa zalla
Sunday Igboho, daya daga cikin masu fafutukar kafa kafa kasar Yarbawa zalla © twitter
Talla

Shaidun gani da ido sun ce harsashin da Yan Sanda suka harba sama domin tarwatsa masu zanga zangar ne ya fada akan matashiyar da ake kira Jimoke wadda ke da shagon sayar da lemon kwalba kusa da wurin taron.

Kungiyar Yan aware ta Yarbawa zalla da ake kira ’Ilano Omo ’O’dua’ dake shirya irin wadannan gangami a jihohin dake kudu maso yammacin Najeriya ta shirya taron na yau a Lagos duk da gargadin da rundunar Yan Sandan Jihar ta yi na kauracewa taron.

Daya daga cikin shugabannin shirya gangamin Sunday Igboho wanda ya sanar da janyewa daga taron sakamakon samamen da jami’an tsaro suka kai gidan sa ya sauya matsayin sa na goyan bayan ci gaba da gangamin.

Igboho ya bukaci magoya bayan sa da suyi watsi da gargadin Yan Sandan wajen halartar gangamin na Lagos, yayin da Yan Sanda suka mamaye inda ska shirya shi.

Ya zuwa wannan lokaci babu wani bayani daga rundunar Yan Sandan Jihar kan abinda ya faru lokacin arangamar da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.