Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Yan bindiga sun sace dalibai 140 a Jihar Kaduna

Wasu Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wata makarantar Sakandare dake karamar hukumar Chikun inda suka kwashe dalibai akalla 140.

Alamun Yan bindiga
Alamun Yan bindiga © India TV News / PTI
Talla

Rahotanni sun ce Yan bindigar sun je makarantar sakandaren da ake kira ‘Bethel Secondary School’ yau da asuba inda suka dinga harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su kwashe daliban ta su gudu da su.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace adadin daliban da aka sace ya kai 140.

Wani malamin makarantar da ake kira Emmanuel Paul yace dalibai 165 suka kwana a makarantar, kuma 25 daga cikin su sun yi nasarar gudu domin kaucewa harin Yan bindigar wadanda suka dauki 140.

Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin amma kuma yace ya zuwa yanzu basu iya tantance yawan daliban da aka kwashe ba.

Wannan harin na zuwa kasa da sa’oi 24 bayan wasu Yan bindigar sun kai hari asibitin da ake kula da kutare da masu fama da cutar tarin fuka a Zaria inda suka kwashe wasu ma’aikatan ta tare da jarirai.

Jihar Kaduna na fama da matsalar Yan bindiga dake kai hare hare makarantu da garuruwa suna kwashe mutane domin karbar diyya.

Ko a jiya kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya sanar da kashe mutane 7 da Yan bindiga suka yi garkuwa da su a kananan hukumomi guda 3 dake Jihar.

Kafin wannan lokaci Yan bindigar sun kai hari kwalejin koyar da aikin noma da Jami’ar Greenfield inda suka kwashi dalibai da dama har sanda aka tattauna da su kafin sakin su.

Gwamnatin Kaduna ta bayyana karara cewar ba zata tattauna ko biya diyya ga duk wasu Yan bindigar dake sace mutane domin karbar diyya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.