Buhari ya likawa shugaban sojin kasa Yahaya sabon mukamin sa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin karawa shugaban hafsoshin sojin kasa Manjo Janar Faruk Yahaya girma zuwa mukamin Laftanar Janar
Wallafawa ranar:
A wani biki da akayi yau a fadar shugaban kasar dake Abuja, Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo sun likawa Yahya sabon mukamin sa na Laftanar Janar a gaban Hafsan Hafsoshin sojin kasar Laftanar Janar Lucky Irabor da shugaban hafsan sojin sama da na ruwa da Sufeto Janar na Yan Sanda da kuma ministan tsaro Janar Bashir Magashi mai ritaya.
A ranar 27 ga watan Mayu shugaba Buhari ya nada Janar Yahaya domin maye gurbin Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu sakamakon hadarin jirgin sama a Kaduna.
Bikin na yau an gudanar da shi ne a fadar shugaban kasa kafin fara taron Majalisar ministoci da aka saba yi kowacce laraba, kuma daga cikin wadanda suka shaida har da shugaban kwamitin soji na Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume.
Shugaba Buhari ya baiwa Janar Yahaya umurnin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi wasu sassan Najeriya musamman na book haram da Yan bindiga barayin shanu da kuma Yan aware.
Najeriya na fuskantar mawuyacin hali a tarihin ta sakamakon tabarbarewar tsaro wanda ke ci gaba da lakume rayuwa daga kusan kowanne sashe na kasar.
Masana harkar tsaro sun bukaci kara yawan jami'an tsaro da kuma kayan aiki na zamani domin tinkarar matsalar, yayin da gwamnonin jihohin kudancin kasar suka bukaci basu damar kafa rundunar Yan Sandan jihohi domin taimakawa jami'an tsaron tarayya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu