Isa ga babban shafi
Najeriya - Ilimi

Iyaye sun koka kan yadda aka gaza ceto 'ya'yansu daga hannun 'yan bindiga

Alkaluma a Najeriya sun nuna cewar yanzu haka akwai dalibai 348 da 'yan bindiga suka sace kuma suke ci gaba da yin garkuwa dasu a jihohin Kaduna, Kebbi da kuma Naija.

Daya daga cikin ajujuwan makarantar sakandaren kimiyya ta garin Kankara dake jihar Katsina, wadda 'yan bindiga suka sacewa dalibai fiye da 300 a ranar 14 ga Disambar 2020.
Daya daga cikin ajujuwan makarantar sakandaren kimiyya ta garin Kankara dake jihar Katsina, wadda 'yan bindiga suka sacewa dalibai fiye da 300 a ranar 14 ga Disambar 2020. © REUTERS/Abdullahi Inuwa
Talla

A jihar Kebbi kawai akwai dalibai 83 da kuma malamai 7 da aka sace daga Kwalejin Gwamnati da ke Birnin Yauri, inda a yanzu haka iyaye da kuma dangin mutanen ke ci gaba da kira ga gwamnati domin ceto su.

Daga birnin na Kebbi wakilinmu El-Yakubu Usman Dabai ya aiko mana da rahoto.

02:48

Rahoto kan makomar dalibai 348 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.