Isa ga babban shafi
Najeriya - Ta'addanci

'Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 348 a Najeriya - UNESCO

Hukumar kyautata ilimi, kimiya da raya al'adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta ce adadin daliban da ‘yan bindiga ke garkuwa dasu yanzu a arewacin Najeriya ya kai 348, bayan da suka sace karin dalibai 121 cikin makon nan a jihar Kaduna.

Daya daga cikin ajujuwan makarantar sakandaren kimiyya ta garin Kankara dake jihar Katsina, wadda 'yan bindiga suka sacewa dalibai fiye da 300 a ranar 14 ga Disambar 2020.
Daya daga cikin ajujuwan makarantar sakandaren kimiyya ta garin Kankara dake jihar Katsina, wadda 'yan bindiga suka sacewa dalibai fiye da 300 a ranar 14 ga Disambar 2020. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

‘Yan bindiga sun sace adadin daliban da suke garkuwa dasu ne daga makarantun dake jihohin Neja, Kaduna da kuma Kebbi, lamarin da hukumar UNESCO tace ka iya tilastawa iyaye janye ‘ya’yansu daga fagen neman ilimi a yankunan da lamarin ya shafa.

Harin baya bayan nan da ‘yan bindiga suka kai kan makaranta a Najeriya shi ne na ranar Litinin da ta gabata, inda suka sace dalibai 121 daga makarantar Bethel Baptist dake Maraban Rido a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.

Allon makarantar Bethel Baptist da 'yan bindiga suka sacewa dalibai 121 a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.
Allon makarantar Bethel Baptist da 'yan bindiga suka sacewa dalibai 121 a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna. © AP

A jihar Kebbi kuwa yanzu haka dalibai 83 ke hannun ‘yan bindigar, kusan makwanni 3 bayan sace jumillar daliban 94 da kuma wasu ma’aikata 8 daga makarantar sakandaren birnin Yawuri. Sai dai sojojin sun samu nasarar ceto dalibai 8 da malami 1 daga cikin waccan adadi, wasu 3 kuma suka rasa rayukansu a yayin da ake kokarin ceto su.

A Jihar Neja kuwa har yanzu ba a kai ga ceto dalibai da malaman Islamiyya 136 ba, da ‘yan bindiga suka sace daga garin Tegina a ranar 30 ga watan Mayu, wadanda ‘yan bindigar suka nemi naira miliyan 100 kafin sakinsu.

Idan muka sake komawa jihar Kaduna kuwa ranar 10 ga watan Yuni, ‘yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai 8 da kuma ma’aikata 2 daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli dake garin Zaria, har yanzu kuma basu sako su ba.

Wasu daga cikin iyayen daliban makarantar sakandaren garin Kankara cikin jimami bayan sace 'ya'yansu da 'yan bindiga suka yi, kafin daga bisani su sako su.
Wasu daga cikin iyayen daliban makarantar sakandaren garin Kankara cikin jimami bayan sace 'ya'yansu da 'yan bindiga suka yi, kafin daga bisani su sako su. © REUTERS/Afolabi Sotunde

Kafin sace-sacen baya bayan nan dai, sai da 'yan bindigar suka taba sace dalibai da dama daga makarantun dake garuruwan Kankara, Kagara da kuma Jangebe a jihohin Katsina, Neja da kuma Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.