Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnonin arewa maso gabas sun dage kan ciyar da shiyar gaba

Gwamnonin shiyar arewa maso gabashin Najeriya, sun gudanar da taron da suka saba yi domin ciyar da shiyar gaba ta fanin tsaro da noma da kuma ci gaban al’ummominsu. Wannan shine karo na biyar da suke gudanar da irin wannan taro a cikin shekaru 2.

Gwamnan jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum ya jagoranci taron bunkasa yankin arewa maso gabashin Najeriya
Gwamnan jihar Barno dake Najeriya Babagana Umara Zulum ya jagoranci taron bunkasa yankin arewa maso gabashin Najeriya RFI hausa/Abba
Talla

Manufar gudanar da wannan taron shi ne kawo karshen matsalar tsaron da ke zama karfen-kafa ga daukacin shiyar.

Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Ahmed Alhassan daga birnin Yola

 

02:59

Gwamnonin arewa maso gabas sun dage kan ciyar da shiyar gaba

Gwamna Baba Gana Zullum na jahar Borno wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ya bayyana cewa, za su tabbatar al’ummarsu a wannan shiyar ta gudanar da harkokinta na yau da kullum cikin tsanaki ba tare da tsoron farmakin ta'addanci ba.

Gwmnan ya kara da cewa "Za kuma mu tabbatar da cewa duk wadanda aka kama da ayyukan ta'addanci an gurfarna da su gaban shari'a kuma an hukunta su kamar yadda ya kamata.”

Bayan taron daya gudana a wannan mako a birnin Jalingo na jahar Taraba, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya shaida wa manema labarai cewa daya daga cikin matsayar da suka cimma ita ce, bukatar samar da sufurin jirgin sama yana mai cewa, Insha Allahu nan da  wata uku za a fara aiki dangane da wannan bangare.

Sai dai har yanzu masana tattalin arziki irinsu Usama Ahmed Dada na ganin cewa, har yanzu akwai sauran rina-a-kaba dangane da bunkasa tattalin arzikin yankin arewa maso gabashin Najeriya ganin yadda 'yan ta'adda ke ci gaba da far wa mutane musamman manoma.

Dada ya ce, 

Ana noma a Barno ana noma a Yobe ana noma a Michika, a yau an saamu tashin hanklai wanda duka manoma sun guji wadannan wurare. Idan ka je noma ko ka noma ko a kashe ka”

Akwai bukatar sake nazarin yadda ake tunkarar harkar tsaro a wannan yankin, ganin yadda aka kwashe shekaru sama da 10 ana fama da rikicin Boko Haram a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.