An gudanar da jana'zar Fasto TB Joshua a Legas
An binne gawar shahararren mai wa’azin kiristancin nan a Najeriya, kuma shugaban cocin Synagogue Church of All Nations (SCOAN), Fasto TB Joshua a Juma’ar nan a harabar cocinsa dake Ikotun a birnin Lagos.
Wallafawa ranar:
Joshua ya rasu ne bayan wata sujadar da aka yi a cocinsa a ranar 5 ga watan Yunin wannan shekarar, kwanaki kadan gabanin zagayowar ranar haihuwarsa, inda zai cika shekaru 58.
Kamfanin dillancin labaran najeriya ya ruwaito cewa mutane daga jinsina, al’adu da kasashe dabam dabam ne suka hallara don bai wa marigayi mai wa’azin girmamawa ta karshe.
Kafin a kai ga sanya shi a rami, an yi addu’o’i tare da karatu da fadakarwa daga littafin Bible mai tsarki.
wanda ya yi wa’azia. jana’izar, Stephen Ogedengbe na ikilisiyar e Wisdom of Chapel Ministry, ya yi kira ga Kiristoci da su yi koyi da halayen TB Joshua don samun salama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu