Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun yi awon gaba da sarkin Kajuru da jikokinsa 13 a Kaduna

‘Yan bindiga sun sace sarkin Kajuru a jihar Kaduna, Alhaji Alhassan Adamu da wasu mutane 13 a fadarsa da safiyar Lahadin nan.

Ayyukan 'yan bindiga na dada kamari a Kaduna, arewacin Najeriya.
Ayyukan 'yan bindiga na dada kamari a Kaduna, arewacin Najeriya. © Social News XYZ
Talla

Rahotanni sun ce an yi awon gaba da sarkin ne da wani basarake, Alhaji Abubakar Kajuru (Salaman Kajuru) da jikokinsa.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun kai samame fadar sarkin ne da asubahin Lahadi, kuma suka ci karensu ba babbaka, har suka dauke sarkin da mutane 13 daga iyalansa.

Ana fargbar abin da ka iya samun sarkin mai shekaru 85 duba da tsufa da ke da nasaba da yawan shekarunsa, inda ake ganin ba zai iya jure takawa a kasa ba.

Wata majiya ta dabam ta tabbatar da cewa a ranar Juam’a sarkin ya kira wani taron gaggawa na tsaro, a kan labarin shirin sace shi.

Ya zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukuma a game da batun sace sarkin na Kajuru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.