Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun harbo jirgin yakin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun harbor jirgin saman yakin rundunar sojin kasar a jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kakkabo jirgin yakin sojojin Najeriya
'Yan bindiga sun kakkabo jirgin yakin sojojin Najeriya AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a wani yanki dake tsakanin jihohin Kaduna da Zamfara lokacin da ake musayar wuta tsakanin sojin saman da ‘yan bindigar.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 da miniti 45 na jiya Lahadi, lokacin da jirgin ke kan hanyarsa ta komawa daga wani harin luguden wuta da ya kai wa ‘yan bindiga a maboyarsu.

Ta cikin sanarwar da rundunar da ta fitar mai dauke da sa hannun daraktan yada labaranta Air Commodore Edward Gabwet, ta ce, matukin jirgin mai suna Abayomi Dairo ya yi nasarar fita da ransa.

A ranar  11 ga watan Mayu, babban hafsan sojin kasar Najeriya Janar  Ibrahim Attahiru da wasu hafsoshin sojin kasar suka mutu sakamakon faduwar wani jirgin saman soji a Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.