Isa ga babban shafi
Najeriya-Igboho

An kama Igboho mai fafutukar wargaza Najeriya

Jami’an tsaron Najeriya sun kama Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa zalla a kasar bayan ya shiga jirgin sama a birnin Kwatano da ke Benin domin tafiya Jamus.

Sunday Igboho
Sunday Igboho © The Cable
Talla

Wani babban jami’n ‘yan sandan Benin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, yanzu haka ana shirye-shiryen tasa keyar Igboho zuwa Najeriya da zarar kasashen biyu sun cimma matsaya kan wasu sharudda.

Tun a farkon wannan wata na Yuli, jami’an tsaron farin kaya na DSS suka yi yunkurin cafke Igboho a gidansa na garin Ibadan a yankin kudancin Najeriya.

Sai dai Igboho ya yi nasarar tserewa a wancan lokaci bayan mukarrabansa da ke ba shi kariya sun shafe tsawon sa’a guda suka musayar wuta da jami’an tsaron.

Jami’an tsaron sun gano wasu kayayyaki a gidan Igboho da suka hada da tarin makamai kamar bindigogi da alburusai, sannan suka kama mutane 12 da kuma wata mace guda.

Wannan na zuwa ne bayan hukumomin Najeriya sun kama Nnamdi Kanu, wanda shi ma ke gwagwarmayar kafa kasar Biafra mai zaman kanta a yankin kudu maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.