Isa ga babban shafi
Najeriya-Jamhuriyar Benin

Alkalin Cotonou ya dage shari'a Sunday Igboho zuwa Litinin

Mai rajin kafa kasar Yarbawa Sunday Adeyemo Igboho, zai sake gurfana gaban alkalin kotu da ke birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin a ranar Litinin mai zuwa bayan da a  Alhamis ya bayyana karon farko a gaban mai shigar da kara na gwamnati, shi da matarsa.

Sunday Adeyemo, mai ikirarin kare hakkin Yarabawa a Najeriya.
Sunday Adeyemo, mai ikirarin kare hakkin Yarabawa a Najeriya. © twitter
Talla

Sunday Igboho da kuma matarsa da yanzu haka ke tsare a hannun jami’an rundunar ‘yan sanda masu yaki da aikata manyan laifufuka da ke birnin Cotonou tun lokacin da aka kama su a farkon wannan mako, za su sake gurfana gaban alkali a ranar litinin mai zuwa don fayyace makomarsu a yunkurin tasa keyarsu zuwa Najeriya.

Wakilain Radio France International a birnin Cotonou Jean-Luc Aplogan, ya ce da farko an gabatar da Igboho da matarsa ne gaban mai shigar da kara na gwamnatin Jamhuriyar Benin a marecen jiya tare da rakiyar lauyoyinsa, kafin daga bisani a sake gabatar da shi gaban wani alkali wanda ya sanar da shi jerin laifufukan da ake zarginsa da aikatawa.

A gaban alkalin, Igboho ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi masa da suka hada da safarar makamai da kuma yunkurin tunzura jama’a da yi wa kasarshi Najeriya tawaye, inda ya ce shi ba dan ta’adda ba ne sannan yana tsoron abin da zai faru da shi idan aka danka shi a hannun mahukuntan Najeriya.

'Yan Najeriya mazauna Cotonou da dama ne suka yi cincirindo a harabar kotun, akwai kuma a wadanda suka ce sun yi tattaki ne daga Lagos don nuna goyon bayansu ga mai fafutukar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.