Isa ga babban shafi
Najeriya-Kebbi

Mafarautan Kebbi sun yi watsi da ceto dalibai don rashin goyon bayan gwamnati

Mafarautan jihar kebbi da suka sha alwashin gano wadanda suka yi garkuwa da daliban makarantar sakandaren birnin Yauri sama da 100  da malamansu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su sun ce sun yi watsi da aikin lalubo yaran  sun saboda rashin goyon baya daga gwamnatin jihar.

Gwamnan jihar Kebbi a Najeriya Abubakar Atiku Bagudu, wanda ya sha alwashin jagorantar mafarauta don ceto daliban Birnin Yauri.
Gwamnan jihar Kebbi a Najeriya Abubakar Atiku Bagudu, wanda ya sha alwashin jagorantar mafarauta don ceto daliban Birnin Yauri. RFI
Talla

A ranar 17 ga watan Yuni ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da daliban makarantar kwalejin gwamnatin Tarayya ta Birnin Yauri.

Sojojin Najeriya sun ce sun ceto 3 daga cikin daliban, kwana guda bayan aukuwar al’amarin, amma suka ce 3 sun mutu yayin aikin ceton.

Kwanaki biyu da suka wuce rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta ceto 2 daga cikin wadannan daliban na Birnin Yauri.

Saura daliban da malamansu na hannun ‘yan bindiga har yanzu, yau tsawon kwanaki 45 kenan, kuma ya zuwa yanzu gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ba su ce komai a game da kokarin da suke na ceto daliban ba.

Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya sha alwashin jagorantar mafarauta zuwa cikin daji don kubutar da wadannan dalibai daga ‘yan bindigar dac suka yi garkuwa da su.

A fusace, jagoran mafarautan jihar Kebbi Abdu bagobiri ya shaida wa manema labarai cewa sun yi watsi da aikin ne saboda watsi da batun da gwamnatin jihar ta yi.

Bagobiri ya ce sun bukaci a ba su motoci da sauran kayan aiki amma har yanzu ba su ga komai ba duk da cewa gwamna ya yi alkawarin samar da duk abin da suke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.