Isa ga babban shafi
NAJERIYA-HADARI

Kotu ta bada umurnin tsare 'dan tsohon shugaban Najeriya saboda kisa

Wata Kotu a Yola dake Najeriya ta bada umurnin tsare ‘dan tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua, wato Aminu Yar Adua a gidan yari saboda tuhumar da ake masa na kashe mutane 4 da mota.

Ministan shariá na Najeriya Abubakar Malami
Ministan shariá na Najeriya Abubakar Malami Daily Post
Talla

Mai gabatar da kara Sufeton Yan Sanda Zakka Musa yace Aminu ya kashe mutanen 4 ne lokacin da yake gudun da ya wuce kima a Yola ranar 23 ga watan Yuni, yayin da wasu mutane 2 kuma suka jikkata.

Daga cikin wadanda Aminu ya banke da mota suka mutu akwai Aisha Umar da Aisha Mamadu da Suleiman Abubakar da kuma Jummai Abubakar.

Mai gabatar da kara yace ‘yan uwan wadanda aka kashe na bukatar naira miliyan 15 a matsayin diyya daga iyalan direban motar Aminu Yar’Adua.

Daga bisani wanda ake zargin yaki amincewa da tuhumar da ake masa na kashe mutanen 4, abinda ya sa mai gabatar da kara ya bukaci kotu ta dage zaman ta domin neman shawara daga ofishin babban mai gabatar da kara dangane da tuhumar.

Daga karshe Mai Shari’a Jummai Ibrahim ta dage zaman kotun zuwa ranar 19 ga watan nan, yayin da ta bada umurnin ci gaba da tsare Aminu Yar ‘Adua.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.