Kwalara ta kashe mutane 60 a Jihar Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina dake Najeriya ta sanar da mutuwar mutane 60 sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar wadda ta kama mutane sama da 1,400.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan lafiyar Jihar Yakubu Danja ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da shugabannin kungiyar likitocin Najeriya a birnin Katsina.
Danja yace yanzu haka gwamnatin na raba maganin yaki da cutar kyauta a asibitocin dake jihar domin dakile yaduwar cutar, tare da kuma shelar yadda jama’a zasu kare kan su daga harbuwa da ita.
A makon jiya hukumomin jihohin Sokoto da Zamfara sun sanar da yawan mutanen da suka mutu sakamakon harbuwa da cutar da suka kai 53, 30 daga cikin su sun mutu ne a Jihar Zamfara, yayin da 23 suka mutu a Sokoto.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu