Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TATTALIN ARZIKI

Gwamnonin Najeriya sun maka Buhari a kotu

Gwamnonin Jihohin Najeriya 36 sun gurfanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gaban kotu saboda zargin da suke yiwa gwamnatin tarayya na karkata kudin da ya kai naira triliyan guda da biliyan dubu 800 daga cikin kudaden da aka kwato daga hannun wadanda suka saci kudaden gwamnati.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Nigeria Presidency/Handout / REUTERS
Talla

Karar da aka shigar a kotun koli ta kuma kunshi karkata akalar kadarorin da kudin su ya kai naira biliyan N450  daga cikin wadanda aka kwato tun daga shekarar 2015.

Jihohin na zargin gwamnatin tarayya da kin biyan wadannan makudan kudade a asusun tarayya da kuma karkata akalar su zuwa wasu asusun ajiya na daban sabanin abinda dokar kasa ta tanada.

Shugaban Gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi
Shugaban Gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi kayodefayemi.com

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewar duk wasu kudaden shigar da kasar ke samu za’a zuba su ne cikin asusu guda ta hanyar da za’a dinga raba su kamar yadda doka ta tanada.

Jihohin Najeriyar na zargin gwamnatin tarayya da yin choge wajen karkata wadannan kudaden domin amfanin kan ta, saboda haka suna bukatar kotun koli da ta bukace ta da ta dawo da kudaden asusun tarayya domin raba su kamar yadda doka ta tanada.

Jihohin sun kuma bukaci gudanar da bincike domin gano yawan kudaden da aka samu daga cikin wadanda ake kwatowa a hannun barayin gwamnati tun daga shekarar 2015 lokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau karagar mulki.

Yan gudun hijirar da rikici ya raba da muhallin su a Nijar
Yan gudun hijirar da rikici ya raba da muhallin su a Nijar © BOUREIMA HAMA/AFP

Gwamnonin a karkashin jagorancin Gwamnan Ekiti kuma shugaban su Kayode Fayemi sun dauki tawagar kwararrun lauyoyi wanda Femi Falana zai jagoranta domin wakilatar su a karar da suka shigar jiya litinin.

Gwamnonin sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da take hakkokin jihohin kasar a daidai lokacin da yace yana yaki da cin hanci da rashawa.

Dokar kasa ta baiwa kotun koli hurumin sauraron kara tsakanin gwamnatocin jihohi da kuma tarayya akan batutuwan da suka shafi kundin tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.