Isa ga babban shafi
RIKICIN-KABILANCI

Gwamna Lalong ya gana da shugabannin kabilar Irigwe da Fulani

Gwamnan Jihar Plateau dake Najeriya Simon Bako Lalong ya bayyana bacin ran sa da tashe tashen hankulan da ake samu tsakanin Yan kabilar Irigwe da Fulani dake karamar hukumar Bassa.

Gwamna Simon Lalong na Jihar Plateau
Gwamna Simon Lalong na Jihar Plateau © PLSG
Talla

Lalong ya bayyana takaicin sa inda ake ci gaba da samun kashe kashe har ya zuwa ranar talatar da ta gabata, inda aka kashe mutane 5 a karamar hukumar bayan sama da 30 da suka mutu a karshen mako duk da dokar hana fita da gwamnati ta kafa.

Yayin ganawa da shugabannin kabilun biyu a fadar gwamnatin jihar, Gwamna ya kuma nuna damuwar sa dangane da yadda ake samun aikata laifuffuka a yankin Bassa wanda ake danganta shi da rikicin kabilanci da addini wanda ya kaiga haifar da rasa rayuka da lalata kadarori da dama.

Shuagbannin Yan kabilar Irigwe
Shuagbannin Yan kabilar Irigwe © PLSG

Sanarwar da Daraktan yada labaran Gwamnan Makut Simon Macham ya rabawa manema labarai tace Lalong ya tabo irin rawar da gwamnatin jihar ta taka wajen sasanta manoma da makiyaya a karamar hukumar Bassa wanda ya kaiga bangarorin sun yi alkawarin zaman lafiya kafin daga bisani su karya shi.

Gwamnan ya bukaci tattaunawa ta hakika tsakanin shugabannin kabilun biyu domin lalubo hanyar kawo karshen kashe manoma da makiyaya da ake samu da kuma lalata gonaki da dabbobin su.

Shugabannin Fulani makiyaya a Jihar Plateau
Shugabannin Fulani makiyaya a Jihar Plateau © PLSG

Babban Basaraken Irigwe, Brra Ngwe Rev Ronku Aka ya shaidawa gwamnan cewar mutanen sa masu son zaman lafiya ne da kuma zama tare da kowa, kuma a shirye suke su ci gaba da zaman lafiya da mazauna yankin cikin su harda Fulani makiyaya wadanda suka kwashe shekaru suna zaman lafiya a tsakanin su.

Brra Ngwe yace babban matsalar dake tsakanin su itace yadda ake lalata gonakin su da kuma kaiwa manoma hari abinda ya talauta su, yayin da ya yiwa gwamnan alkawarin cewar duk da matsalolin da aka samu a shirye suke su yafewa juna domin ci gaba da zama da kowa cikin su harda Fulani.

Basaraken ya bukaci kara yawan jami’an tsaro a yankin na su, yayin da yayi alkawarin taimakawa wajen gano bata garin dake cikin masarautar sa.

Brra Ngwe ya kuma bukaci gwamnan da ya taimakawa wadanda suka samu raunuka da wadanda suka suka rasa matsugunin su tare da wadanda suka rasa gonakin su.

Shi kuwa shugaban kungiyar Fulani makiyaya Alh Nuru Abdullahi yace duk da yake Fulani sun dauki dogon lokaci suna zama a karamar hukumar Bassa suna fama da matsalar kai musu hari ana kashe su da sace musu dabbobin su.

Abdullahi yace ana amfani da batun rikicin manoma da makiyaya ne kawai domin aikata laifuffuka wajen satar shannun su, saboda haka ya dace jami’an tsaro su zakulo wadanda suka kashe Yan kabilar Irigwe da Fulani da masu lalata gonakin su da kuma satar shanu domin hukunta su.

Shugaban Fulanin yayi alkawarin ci gaba da zaman lafiya da sauran al’ummomin dake yankin da kuma taimakawa wajen zakulo masu aikata laifuffuka a cikin su.

Daga bisani Gwamna Lalong ya sha alwashin cewar gwamnatin sa zata duba bukatun da suka gabatar wajen aiwatar da su, yayin da yayi bayyana cewar nan bada dadewa ba gwamnatin jihar zata aiwatar da shirin makiyaya wanda zai kaiga samar da wuraren kiwo da kuma kasuwancin dabbobi wanda yace zai taimaka wajen rage rikice rikicen da ake samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.