Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Fulanin Taraba sun mika masu garkuwa da mutane a cikin su

Shugabannin kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya sun mika wasu mutane 11 da ake zargin cewar masu garkuwa da mutane ga rundunar Yan Sandan Jihar Taraba.

Wasu da ake zargi da laifin garkuwa da mutane a Taraba
Wasu da ake zargi da laifin garkuwa da mutane a Taraba © Daily Trust
Talla

Shugaban kungiyar Sahabi Tukur ya bayyana cewar sun yi haka ne sakamakon alkawarin da suka yiwa Sarkin Muri Abbas Tafida na tona asirin wadanda ke aikata irin wannan laifi a cikin su.

Tukur yace sun kafa wani kwamiti a tsakanin su da ya kunshi bangarorin Fulanin dake Jihar da za suyi aiki da Yan sanda a kananan hukumomi 16 domin zakulo masu garkuwa da mutane da kuma aikata wasu laifuffuka.

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Abimbola Sokoya ya yaba da matakin da kungiyar ta dauka na shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Sokoya ya kuma bukaci samun hadin kai tsakanin Jihohin Adamawa da Benue da kuma Taraba domin dakile ayyukan garkuwa da mutane da wasu laifuffukan da suka addabi jama’a, yayin da ya sha alwashin baiwa Fulanin goyan bayan samun nasara.

Wasu masu garkuwa da mutane guda 6 da suka tuba a wurin, an basu Alkur’ani sun rantse cewar ba zasu aikata laifin ba ko kuma satar shannun jama’a.

A watannin da suka gabata Sarkin Muri Abbas Tafida ya sha alwashin daukar mataki mai tsauri na kashe ‘yan uwan mutanen da suka addabe su wajen garkuwa da mutane ko satar shannu ko kuma kashe jama’a a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.