Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

'Yan bindiga sun kai hari Cibiyar horar da sojin Najeriya ta NDA

'Yan bindiga a Najeriya sun kutsa kai barikin Babbar Cibiyar horar da hafsoshin sojin kasa ta NDA inda suka kashe wasu sojoji 2 da kuma sace wasu da ake kyautata zaton manyan hafsoshi ne masu mukamin manjo guda 2.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo suna likawa Laftanar Janar Faruk Yahaya, shugaban sojin kasa sabon mukamin sa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo suna likawa Laftanar Janar Faruk Yahaya, shugaban sojin kasa sabon mukamin sa © Nigeria presidency
Talla

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar 'Yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 1 na dare, kuma har zuwa safiyar yau suna cikin barikin.

Jaridar tace wata majiya ta shaida mata cewar jami’an tsaro sun yiwa makarantar kawanya domin hana 'Yan bindigar tserewa tare da wadanda suka kama, yayin da ake cikin zulumi akan yadda suka yi nasarar kutsa kai ciki Cibiyar.

Majiyar tace an rufe duk wata hanya dake amfani da ita wajen shiga Cibiyar domin gudanar da bincike, yayin da aka kai daya daga cikin ofishoshin da suka samu rauni zuwa asibitin dake cikin barikin.

kakakin Cibiyar Manjo Bashir Muhammed Jajira ya tabbatar da rahotan kutsen da aka musu tare da kashe jami'an su guda biyu da kuma raunata guda, yayin da aka dauke guda.

Hare haren 'Yan bindiga sun zama ruwan daren a yankin arewacin Najeriya musamman jihohin Kaduna da Zamfara da Katsina da Niger inda yanzu haka ake rike da mutane da kuma Dalibai da dama da akayi garkuwa da su.

Ya zuwa yau daliban makarantar Islamiyar Salihu Tanko dake Tegina sun kwashe kwanaki 86 a hannun Yan bindigar da na Kwalejin Birnin Yawuri da suka kwashe kwanaki 69 sai na kwalejin Bethel da suka kwashe kwanaki 51.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.