Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Majalisar dokokin Plateau ta baiwa Gwamna Lalong wa'adin makwanni biyu

Majalisar dokokin Jihar Plateau dake Najeriya ta baiwa Gwamna Simon Lalong wa’adin makwanni biyu da ya dauki mataki akan kashe kashen da ake samu a jihar ko kuma ta dauki nata mataki akan sa, yayin da ta bukaci jama’ar jihar da su kare kan su.

Gwamna Simon Lalong na Jihar Plateau
Gwamna Simon Lalong na Jihar Plateau © PLSG
Talla

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dasun Phili Peter ya bayyana cewar jami’an tsaron hukuma sun gagara kare lafiyar jama’ar jihar, saboda haka suna bukatar mutane su tashi domin kare kan su.

Peter yace Majalisar ta baiwa Gwamna Lalong wa’adin makwanni biyu da yayi aiki da shawarwarin da ta bashi akan yadda za’a dawo da zaman lafiyar a jihar, idan kuma yaki Majalisar zata dauki matakin da ya dace.

Shugaban kwamitin yada labaran ya bukaci jami’an tsaro da su zakulo wadanda suka aikata kisan gilla a jihar domin hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Hotan Gwamna Lalong na ganawa da hukumomin tsaro
Hotan Gwamna Lalong na ganawa da hukumomin tsaro RFI hausa

Peter ya jajantawa gwamnati da jama’ar jihar saboda abinda ya kira kisan tashin hankalin da aka gani a kananan hukumomin Bassa da Barikin Ladi da Bokkos da Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Mangu da Riyom da kuma na baya bayan nan da aka samu a Yelwa Zangam da Jami’ar Jos.

Shugaban kwamitin yace Majalisar tayi Allah wadai da daukacin kisan gillar da aka samu wanda yace ba abinda zasu amince da shi bane, yayin da ya aike da sakon ta’aziya ga iyalan wadanda aka kashe.

Gwamna Simon Lalong na zagaya wani sashe na birnin Jos tare da shugabannin hukumomin tsaro
Gwamna Simon Lalong na zagaya wani sashe na birnin Jos tare da shugabannin hukumomin tsaro © PLSG

Peter yace suna kira ga mutanen Jihar Plateau da su tashi tsaye domin kare kan su da al’ummomin su, domin jami’an tsaron da ake da shi ba zasu iya kare su ba.

Daga nan sai ya yabawa matasan Jihar dangane akan yadda suka hada kan su wajen nuna rashin amincewar su da kashe kashen da kuma yadda suka yada hotunan gawarwakin wadanda aka kashe a kafofin sada zumunta domin duniya ta gani.

Dan majalisar ya kuma ce suna dakon sanarwa daga Gwamna Lalong da shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da mutanen da aka kashe a Yelwa Zangam kamar yadda suka yi bayan kashe matafiya a hanyar Rukuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.