Isa ga babban shafi

Najeriya na tunanin fara daukar matakin tilastawa ‘yan kasar karbar allurar Korona

Mahukunta Najeriya sun bayyana cewa suna tunanin fara daukar matakin tilastawa ‘yan Kasar karbar allurar rrgakafin hana kamuwa da cutar COVID 19, ganin yadda cutar ke kara bazuwa a fadin kasar, sakamakon sake dawowar ta a karo na uku.

Allurar Moderna
Allurar Moderna Josep LAGO AFP/Archivos
Talla

A duk kullum Hukumomin Najeriya na fitar da alkaluma dangane da mutanen da cutar ke kashewa sakamakon harbuwa da cutar korona .

Hukumomin Najeriya sun tabbatar da samun karuwar mutanen dake harbuwa da nauyin cutar da aka yiwa lakabi da Delta musamman a birnin Lagos mai yawan jama’a.

Jami'in kiwon lafiya dake yaki da cutar Covid 19
Jami'in kiwon lafiya dake yaki da cutar Covid 19 Getty Images - Ezra Acayan

Alkaluman da hukumomin suka gabatar sun nuna cewar daga cikin mutane 650 da suka kamu da cutar a ranar asabar, 261 sun fito ne daga birnin Lagos, sai Jihar Ondo mai mutane 95 sannan Rivers mai mutane 80.

Allurar rigakafin cutar  Covid na Pfizer
Allurar rigakafin cutar Covid na Pfizer Robyn Beck AFP

Sauran jihohin da aka samu masu dauke da cutar sun hada da Akwa Ibom mai mutane 59, sannan Oyo mai mutane 24, sai kuma Ekiti mai mutane 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.