Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Najeriya ta zargi kungiyar Amnesty da goyawa 'yan ta'adda baya

Gwamnatin Najeriya tayi zargin cewar haramcaciyar kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra ta tara tarin bama bamai a sassan kasar domin gudar da ayyukan ta da su, sabanin yadda kungiyar Amnesty International ke kare ayyukan ta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da haka a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai a matsayin martani ga rahotan kungiyar Amnesty International wanda ya zargi jami’an tsaron kasar akan yadda su ke tinkarar masu fafutukar kungiyar a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Sanarwar tace duk da ikrarin kungiyar Amnesty na rashin daukar bangare a harkokin siyasar Najeriya, tayi dumu dumu wajen shiga harkokin siyasar kasar a daidai lokacin da take gudanar da ayyukan ta.

Shehu yace ana amfani da kungiyar Amnesty domin cimma wata manufa, wanda yace wannan ba wani sabon abu bane a Afirka, ganin yadda take ikrarin rashin nuna bangaranci amma kuma ayyukan ta sun saba da haka.

Sojojin Najeriya dake yaki da Yan ta'adda
Sojojin Najeriya dake yaki da Yan ta'adda Audu Marte AFP/Archivos

Kakakin shugaban kasar yace kungiyar Amnesty International bata da hurumin ci gaba da zama a Najeriya, inda ya bukace ta da ta kaddamar da bincike akan masu mata aiki a ofisoshin ta dake kasar, domin yiwa kanta kwaskwarima akan yadda take gudanar da harkokin ta.

Shehu yace gwamnatin Najeriya zata ci gaba da yaki da ta’addanci ta kowacce hanya, kuma ba zata saurari korafin da kungiyar Amnesty ke yi ba, musamman ganin yadda kungiyar bata aiwatar da abinda take bukatar ganin wasu sun yi.

Kakakin shugaban ya zargi kungiyar da goyawa ‘Yan ta’adda baya, sabanin wadanda ake takewa hakki wajen raunata su da raba su da matsugunan su da kuma hallaka su baki daya.

Jagoran masu fafutukar kafa Biafra a kudancin Najeriya Nnamdi Kanu, lokacin da ya gurfana a gaban kotu a shekarar 2015
Jagoran masu fafutukar kafa Biafra a kudancin Najeriya Nnamdi Kanu, lokacin da ya gurfana a gaban kotu a shekarar 2015 AP - AP Photo

Shehu yace kungiyar IPOB ta hallaka Yan Najeriya da dama cikin su harda jami’an Yan Sanda da soji tare da bankawa ofisoshin gwamnati wuta tare da tara makaman da suka hada da bama bamai a fadin Najeriya, amma Amnesty taki cewa komai akai.

A ranar 5 ga watan Agustan da ta gabata, kungiyar Amnesty ta fitar da wata sanarwa wadda ta zargi jami’an tsaron Najeriya da kashe fararen hula 115 a Yankin kudu maso gabas, ba tare da cewa komai akan jami’an tsaron da ‘yayan kungiyar suka kashe ba.

Daraktar kungiyar a Najeriya Osai Ojigbo tace bayanan da suka tattara sun nuna yadda jami’an tsaron Najeriya ke amfani da karfin da ya wuce kima a jihohin Imo da Anambra da kuma Abia domin murkushe ‘yayan kungiyar IPOB da ESN da ake zargi.

Amnesty tace binciken ta ya nuna mata laifuffuka 52 da akayi a jihohin Anambra da Imo da Ebonyi da kuma Abia wadanda suka kai 62 dake da nasaba da cin zarafi da azabtarwa da kuma kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.