Isa ga babban shafi
Najeriya - Maiduguri

Al'ummar Barno sun zargi gwamnati da gazawa wajen barinsu cikin duhu

A jihar Borno da ke Tarayyar Najeriya, yanzu haka jama’a sun share tsawon watanni 8 ba tare da wutar lantarki ba, wannnan kuwa bayan da mayakan Boko Haram suka lalata wasu manyan turakun wutar lantarki da ke sada jihar da sauran sassan kasar.To sai dai tuni wasu suka fara zargin gwamnatin jihar ta Borno da kin daukar matakan da suka wajaba don magance wannan matsala. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahoton wakilinmu Bilyamin Yusuf daga Maiduguri.

Turakun wutar lantarki a Najeriya.
Turakun wutar lantarki a Najeriya. © Ventures Africa
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.