Najeriya - Buhari
Buhari ya sake umurtan jami'an tsaro wajen kawo karshen 'Yan bindiga
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci rundunonin Sojin Kasar da su bullo da sabbin hanyoyin yakin da suke yi don murkushe ‘yan Ta’addan da ke garkuwa da jama’a a yankin Arewa maso yamma da Arewa ta Tsakiya cikin gaggawa. Bayyani sun ce a cikin makon nan ne Najeriya za ta sake samun Karin jiragen yaki kirar Super Tucano domin kawo karshen Ta’addanci a fadin kasar. Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahoton da wakilinmu Kabiru Yusuf ya aiko mana daga Abuja.
Wallafawa ranar:
Minti 2
Kunna - 01:29