Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Sama da muggan makamai dubu 60 na hannun 'yan bindiga a arewacin Najeriya

Wani rahoton bincike bincike a Najeriya ya bayyana cewar adadin muggan makaman da ke hannun ‘yan bindiga da sauran miyagun mutane a yankin arewa maso yammacin kasar sun zarta dubu 60.

'Yan bindiga sun addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya
'Yan bindiga sun addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya © dailypost
Talla

Dakta Muratala Ahmed Rufa’i malami a sashin nazirin tarihi na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke jihar Sokoto ne ya bayyana haka cikin binciken da ya shafe akalla shekaru 10 yana yi kan matsalar ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Zuzzurfan binciken da ya yi wa take da ‘I am a Bandit’ ya ce tuni matsalar tsaron ta zamewa wasu ciki hra da ‘yan bindigar hanyar samun kudade la’akari da safarar makaman da suke yi wa miyagun, wadanda suka hada da makaman roka, bindigogin zamani masu sarrafa kansu, AK 47 da kuma AK49.

Dangane da kudaden da ake samu daga safarar makaman kuwa, binciken ya ce ‘yan bindigar na amfani da su wajen sayen miyagun kwayoyi, caca, wayoyin hannu, mata da sauran bukatu da dama.

A cewar Dakta Murtala Rufa’i ya samu bayanan bincikensa ne daga hirarrakin da ya samu damar yi da wasu daga cikin ‘yan bindigar, da wasu mutanen da tashin hankalin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.