Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Daliban Sakandiren Yauri sun cika kwanaki 90 a hannun 'yan bindiga

A Najeriya, daliban sakandiren Yauri sun cika kwanaki 90 a hannun ‘yan bindigar jihar Kebbi yayinda takwarorinsu na kwalejin Bethel a Kaduna ke cika kwanaki 72 dai dai lokacin da dakarun Sojin kasar ke ci gaba da luguden wuta a dazukan Zamfara a wani yunkuri na kawo karshen matsalar ‘yan bindigar da ta dabaibaye kasar.

Wani dakin karatun makarantar Sakandire a Najeriya.
Wani dakin karatun makarantar Sakandire a Najeriya. © REUTERS/Abdullahi Inuwa
Talla

Daliban Sakandiren ‘yan Mata ta yawuri 30 ne yanzu haka ke ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan bindigar daji tsawon kwanaki 90, duk da kiraye-kirayen iyaye ga gwamnatoci da kuma yunkurin kundumbalar da wasu suka kudiri niyyar yi bayan bayanan da ke cewa daliban yanzu haka na cikin dajin Rijau na jihar Neja.

A bangare guda suma daliban kwalejin  Bethel na Kaduna 31 na hannun ‘yan bindigar Dajin, bayan sakin 47 a watan jiya, wadanda zuwa yanzu suka cika kwanaki 72 a tsare.

Matsalar garkuwa da mutane don neman fansa ta zama ruwan dare a arewacin Najeriyar inda lamarin ya fi tsananta a jihohin Kaduna, Zamfara, Neja da kuma Kebbi baya ga jihar Katsina ko da tuni mahukuntan kasar suka fara daukar matakin kawo karshen matsalar bayan luguden wutar Soji a jihar zamfara.

Wasu alkaluma sun nuna yadda ‘yan bindigar dajin suka yi garkuwa da mutane dubu 2 da 371 cikin watanni shidan farkon shekarar nan a jihohin arewa maso yammacin Najeriyar galibinsu dalibai yayinda suka hallaka wani kaso mai yawa a mabanbantan hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.