Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kai hari wata mujami'a a Kogi tare da kashe mutum daya

Wasu ‘yan bindiga a Najeriya sun kai hari kan wani Cocin ECWA da ke Okedayo a jihar Kogi da sanyin safiyar Yau, inda suka kashe mutum daya sannan suka yi garkuwa da mutane biyu.

Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga.
Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga. © PHOTO/FOTOSEARCH
Talla

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun mamaye cocin ne a lokacin da suke hidiman ibada.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP William Ayah, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce wadanda suka samu raunuka a harin suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba. Ya ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na ganin an kamo wadanda suka aikata wannan aika -aika da kuma kubutar da wadanda aka sace.

Amma, ya yi kira ga mutane da su bai wa 'yan sanda bayanai masu amfani da za su kai ga cafke' yan bindigar.

Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Rt. Hon. (Prince) Matthew Kolawole, ya yi Allah wadai da lamarin tare da yin kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu.

Harin cocin na zuwa ne kasa da mako guda bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe sojoji da' yan sanda a wani gidan yari da ke Kabba dake jihar ta Kogi.

Rahotanni sunce an saki fursunoni sama da 200 a harin amma hukumomi sun ce an sake kamo sama da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.