Isa ga babban shafi

Birtaniya za ta yi sassauci ga 'yan Najeriya masu neman zuwa kasar

Babbar jami’ar  kasar Birtaniya dake aiki a Najeriya,  jiya asabar ta bayyana cewa kasar ta daga ranar 4 ga watan Oktoba za ta kawo sassauci dangane da matakan da ta dau da suka shafi yaki da cutar  Covid 19 ga matafiya zuwa Birtaniya.

Takardar dake tabbatar da an yiwa mutum allurar Covid 19
Takardar dake tabbatar da an yiwa mutum allurar Covid 19 © RFI/Privilege Musvanhiri
Talla

Catriona Laing ta ce ba za a sake fuskantar wata matsalla da ta shafi allurar da ake yiwa jama’a  a Najeriya da zaran suke da niyar zuwa Birtaniya.

Allurar rigakafin Cutar Covid 19
Allurar rigakafin Cutar Covid 19 AFP - RODRIGO BUENDIA
Jami’ar ta ce Birtaniya ta amince da alluran Oxford Astra Zeneca,Moderna,Pfizer da Johnson& Johnson da ake  yiwa  jama daga Najeriya.
Allurar Pfizer
Allurar Pfizer AP - Rogelio V. Solis
Kasar ta Birtaniya ta taimakawa Najeriya da allurai kusan milyan daya da dubu dari biyu a shiri na Covax ,kuma za ta ci gaba da  kawo na ta gundumuwa zuwa Najeriya  na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.