Isa ga babban shafi
Najeriya

Damar taimaka wa talaka ta kare wa Buhari - Kwande

Tsohon Jakadan Najeriya a Switzerland kuma wanda ya yi aiki tare da Sardauna, Sir Ahmadu Bello, wato Yahaya Kwande ya bayyana cewa, babu wani sauran lokaci da ya rage wa shugaba Muhammadu Buhari domin taimakon talakan Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS - Siphiwe Sibeko
Talla

Ambasada Kwande ya bayyana haka ne a yayin wata hira da musamman da sashen Hausa na RFI albarkacin cikar Najeriya shekaru 61 da samun 'yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya.

Tsohon jakadan ya bayyana cewa, a halin yanzu, Buhari ba ya tunanin talaka domin kuwa ta kanshi yake.

Yanzu shi ma tunani yake yi kan abin da zai yi bayan ya kammala, ba yana tunanin talakawa ba ne, abin da bai yi ba a shekaru bakwai da suka gabata, me zai iya yi cikin shekara guda, domin lokacin da ya kamata ya taimaki kasar nan an ba shi shekaru takwas kuma ta kare. Inji Kwande

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar Ambasada Kwande tare da wakilinmu na Jos, Tasiu Zakari.

 

03:27

Damar taimaka wa talaka ta kare wa Buhari - Kwande

 

Tsohon Jakadan ya kara da cewa, a halin yanzu ba ya tutiyar cewa shi dan Najeriya ne ganin yadda al'amura suka lalace a kasar, inda zubar da jini ta zama ruwan dare tamkar babu gwamnati a kasar.

Tsohon Jakadan Najeriya a Switzerland a zamanin mulkin Sardauna, Amsada Yahaya Kwande
Tsohon Jakadan Najeriya a Switzerland a zamanin mulkin Sardauna, Amsada Yahaya Kwande © Tribune

Haka kuma ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta sanya talakawa a gaba, yana mai bada misalin yadda farashin abubuwa suka yi tsada kamar magani.

Har ila yau tsohon jakadan ya bayyana irin yadda talakan Najeriya ke yi wa gwamnati biyayya a zamanin mulkin Sardauna saboda gwamnatin wancan lokacin ta damu da shi ba kamar yadda al'amura suka sauya ba a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.