Isa ga babban shafi
Najeriya

Faransa za ta taimaka wa Najeriya wajen magance matsalar tsaro

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alkawarin zurfafa zumunci tsakanin kasarsa da Najeriya, musamman ma ta wajen tinkarar matsalar tsaro.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron  tare da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari. Ludovic MARIN / POOL / AFP
Talla

Hakan na kunshe ne a wata sanarwar da Macron din ya aike wa shugaba Muhammadu Buhari, ta ofishin jakadancin Faransa a Najeriya,  don taya shi murnar tunawa da cikar kasar shekaru 61 da samun yancin kai.

A cikin sanarwar Macron ya jaddada kudirinsa na yaukaka zumunci tsakanin Faransa da Najeriya, wanda zai kai ga habakar tattalin arziki da bunkasar al’umma.

Shugaban na Faransa ya ce tun bayan da ya ziyarci kasar a shekarar 2018, dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa na ci gaba da habaka, musamman ma a fannin tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.