Isa ga babban shafi
Najeriya-Zabe

Sanin yankin da dan takarar 2023 zai fito ne zai fayyace makomar PDP- Atiku

Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya ce sanar da yankin da ‘dan takarar shugaban kasar zaben shekarar 2023 zai fito ne zai nuna makomar Jam’iyyar su ta PDP mai adawa a zabe mai zuwa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar. REUTERS/Tife Owolabi
Talla

Atiku ya ce Jam’iyyar na da hurumin amincewa da dokokin ta, da kuma yadda za a tafiyar da ita, yayinda su kuma ‘yan Najeriya ke da hurumin zabin wanda su ke so ya jagorance su lokacin gudanar da zabe.

Tsohon mataimakin shugaban kasar na daga cikin ‘yayan Jam’iyyar PDP da ke shirin shiga takarar zaben na shekara 2023, yayin da ake hasashen cewar Jam’iyyar na iya bai wa yankin kudancin kasar damar tsayar da ‘dan takara, ganin cewar mulkin Najeriyar zai cika shekaru 8 a hannun shugaba Muhammadu Buhari da ya fito daga yankin arewa.

Atiku ya ce a shekarar 2003 gwamnonin PDP sun sa shi tsayawa takarar domin hana shugaba Olusegun Obasanjo zarcewa, amma yaki tsayawa, abinda ya bai wa shugaban damar samun nasara.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce babu wani abu da ake kira shugaban kudancin Najeriya ko kuma shugaban arewacin Najeriya, sai dai shugaban Najeriya kawai, saboda haka matakin da jam’iyyar za ta dauka ya na da matukar tasiri dangane da makomar ta.

Rahotanni sun ce Jam’iyyar PDP ta bai wa Yankin arewacin Najeriya damar fitar da dan takarar shugabancin ta, abinda ke nuna cewar ‘dan takarar shugaban kasa na iya fitowa daga yankin kudu.

Jam’iyyar PDP ta kwashe shekaru 16 tana jagorancin Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2015 kafin APC ta raba ta da mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.