Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SIYASA

Babu 'dan siyasar da ya kai Buhari farin jini a raye - Osinbajo

Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin ‘dan siyasar da yafi kowa farin jini a tsakanin al’ummar kasar dake raye a wannan lokaci.

Shuagaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shuagaban Najeriya Muhammadu Buhari © John Angelillo / Pool / REUTERS
Talla

Osinbajo yace farin jinin shugaban da kuma gaskiyar sa na da matukar tasiri wajen shawo kan matsalolin da suka addabi kasar.

Mataimakin shugaban yace Buhari ne kawai zai ziyarci wuri ba tare da tilastawa jama’a ba, amma kuma kaga daruruwan mutane sun taru domin ganin sa ko sauraron sa.

Osinbajo dake jawabi a birnin London lokacin da ya halarci wani taro, yace suna bukatar kima irin na shugaban kasar domin shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya.

Mataimakin shugaban yace wannan ya sa duk da matsalolin da ake fuskanta, shugaban ne kawai kan iya kiran kowa, ciki harda wadanda basu yarda da manufofin sa amma su taho da gudu.

Osinbajo yayi gargadi akan masu bukatar raba Najeriya, inda yake cewa yanzu haka kananan kasashe na neman hadewa da wasu domin kara karfin su, saboda haka babu dalilin raba Najeriyar.

Mataimakin shugaban ya kawo misali da manyan kabilun kasar irin su Yarbawa da Igbo da kuma yankin arewacin kasar inda yake cewa babu wata al’umma da zata ci gaba ita kadai, saboda haka ya dace a ci gaba da dorewar Najeriya a matsayin kasa guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.