Isa ga babban shafi
ZABEN-APC

Rikicin cikin gida ya mamaye Jam'iyyar APC

Bisa dukkan alamu ana iya cewa rikicin cikin gida na ci gaba da tasiri a Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, ganin yadda aka gudanar da tarurruka mabanbanta a wasu Jihohin kasar domin zaben shugabannin da zasu jagorance ta a matakan jihohi.

Shugaban Jam'iyyar APC na riko Mai Mala Buni
Shugaban Jam'iyyar APC na riko Mai Mala Buni © Daily Nigerian
Talla

A Jihar Kano, rahotanni sun ce bangaren Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayan sa sun zabi Alh Ahmadu Haruna Zago a taron da suka gudanar, yayin da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da Kabir Gaya ke gudanar da nasu taron inda ake saran zaben Abdullahi Abbas a matsayin shugaba.

A Jihar Lagos ma, barakar ta fito fili, inda wani bangare na Jam’iyyar ya gudanar da taron sa a Agege, inda ya bayyana Hon Sunday Ajayi a matsayin shugaba, yayin da bangaren Bola Ahmed Tinubu ya amince da jagorancin Hon Cornelius Ojelabi.

Mawaka na jinjinawa jagoran APC Bola Ahmed Tinubu
Mawaka na jinjinawa jagoran APC Bola Ahmed Tinubu © Joe Igbokwe

A Jihar Ogun an ce wasu ‘Yan bindiga sun kai hari akan masu gudanar da taron jam’iyyar, inda acan ma ake da bangarori biyu tsakanin masu goyan bayan Gwamna Dapo Abiodun da kuma masu goyan bayan tsohon Gwamna Ibikunle Amosun.

A jihar Nasarawa, Jam’iyyar ta amince da sasantawa a tsakanin kananan hukumomin jihar domin raba mukaman ta tsakanin bangarorin jihar.

Gwamnan Borno Babagana Zulum da wadanda suka gabace shi  Kashim Shettima da Ali Modu Sheriff
Gwamnan Borno Babagana Zulum da wadanda suka gabace shi Kashim Shettima da Ali Modu Sheriff © Daily Nigerian

A jihar Borno, an ga Gwamna Babagana Umara Zulum da wadanda ya gada Kashim Shettima da Ali Modu Sherrif na halartar taron jam’iyyar wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali.

Wadannan shugabannin jam’iyyar da za’a zaba yau ake saran su jagorance ta wajen tsayar da ‘yan takarar zaben Gwamna da ‘Yan Majalisu da kuma shugaban kasar da za’ayi a shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.