Najeriya - 'Yan bindiga
'Yan bindiga sun sace tagwaye 'ya'yan wani sarki a Kwara
Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun yi garkuwa da tagwaye biyu mata 'ya'yan wani basarake a Jihar Kwara, Oba Samuel Adelodun.
Wallafawa ranar:
Talla
Kazalika maharan sun yi awon gaba da masu yi masa hidima uku, kamar yadda Kakakin 'Yan Sandan Kwara Cp Okasanmi Ajayi ya tabbatar.
An bayyana waɗanda aka sace a matsayin direban sarkin da mai tsaron lafiyarsa, da kuma 'yar aikin gidan.
A cewar Kakakin ‘Yan sandan, mutanen na kan hanyarsu ta zuwa Obbo Ayegunle daga Osi kafin su ci karo da 'yan bindigar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu