Isa ga babban shafi
Coronavirus-Najeriya

Kashi 84 na 'yan Najeriya basu da tanadin yaki da covid-19- UNICEF

Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin duniya UNICEF ya ce kashi 84 na ‘yan Najeriya ba su iya tanada kayayyakin wanke hannaye a gidajensu da wajen ayyukansu ba. Yayin da kaso 9 daga cikin 10 na Makarantun Kasar, suma ba su iya tanadarwa dalibansu wajen wanke hannayen ba. Dukkuwa da yadda kasar ke yaki da cutar COVID 19 da sauran cututtuka masu yaduwa. Ga rahotan da wakilin mu Muhammadu Kabiru Yusuf ya aiko mana.

Wani wajen wanke hannu a kasuwar Mushin da ke jihar Lagos.
Wani wajen wanke hannu a kasuwar Mushin da ke jihar Lagos. © AFP - Pius Utomi Ekpei
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.