Isa ga babban shafi
Najeriya-Nnamdi Kanu

Babbar Kotun Najeriya ta fara shari'ar Nnamdi Kanu a Abuja

Babbar Kotun Najeriya da ke Abuja ta fara zaman saurarar karar jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu wanda ya isa kotun da safiyar yau bisa rakiyar jami’an tsaro fiye da 65.

Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Tuni dai kotun ta fara shari’ar ko da ya ke an haramtawa 'yan jarida shiga cikin kotun.

Rahotanni sun ce jami’an da suka yi rakiyar Kanu zuwa kotun har da DSS da ‘Yan sanda da kuma Civil Defense a motoci 10.

Wasu ganau sun ce jami’an DSS da su ke cikin rakiyar ta Kanu na rike da manyan makamai yayinda wasu motocin ‘yan sandan kwantar da tarzoma na daban suma suka yiwa kotun kawanya.

Guda cikin jami’an na DSS ya fara yiwa ‘yan jarida bayanin cewa baza su samu izinin iya shiga cikin kotun ba, yayinda jami’an suka sanya shingaye.

Nnamdi Kanu wanda ke tsare hannun hukumomin Najeriya tun bayan kamo shi daga ketare ya na fuskantar tuhume-tuhume 7 ciki har da na ta’addanci da cin amanar kasa da kuma cin mutuncin shugaban kasa baya ga tunzura jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.