Isa ga babban shafi
najeriya - ipob

Najeriya ta yi kira ga kasashen da ke goyan bayan Nnamdi Kanu da su daina

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga kasashen da ake zargin na goyon bayan Nnamdi Kanu, da haramtaciyarsa ta ‘Yan asalin Biyafara (IPOB), da su daina.

Jagoran haramcecciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu, 26/05/2017.
Jagoran haramcecciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu, 26/05/2017. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Ministan shari’a kuma babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, ya ce irin wadannan kasashe na tallafa wa ayyukan Kanu, da IPOB, duk da sun kwana da sanin cewa gwamnati da ayyana kungiyar a matsayin ta ta’addanci a Najeriya.

Mista Malami wanda ya kira taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja jiya Jumma’a kana daya bayan da aka gabatar da Mista Kanu don sake gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi cin amanar kasa da ta'addanci.

Jawabin nasa ya ta'allaka ne kan rahoton binciken da kwamitin wucin gadi na shugaban kasa mai membobi 24, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar, biyo bayan tsare Kanu a wajen Najeriya a watan Yuni.

IPOB ta kashe jami'an tsaro 175

Kwamitin wanda Mista Malami ke jagoranta ya alakanta “ayyukan barna” daban -daban da suka hada da kisan manyan mutane da jami'an tsaro 175, lalata ofisoshin 'yan sanda kusan 164, da sauran manyan laifuka kan IPOB da reshenta ta (ESN).

Zanga-zangar Endsars

IPOB da ESN sun kai hare-hare da dama da lalata dukiyoyin jama'a lokacin zanga-zangar EndSars da kuma zanga-zangar masu neman ƙasar Biafra a yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudu musamman fadar Oba na Lagos da gidan gwamnan Imo Sanata Hope Uzodinma da kuma ƙone motoci 150 a tashar motocin fasinja na Oyigbo dake Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.