Najeriya za ta kaddamar da Nairar yanar gizo ta eNaira
A Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da Nairar da za a rika hada hada da ita ta intanet, wato eNaira, a fadarsa da ke babban birnin kasar Abuja, a cewar wata sanarwa da ta fito daga babban bankin kasar ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne bayan da aka jinkirta kaddamar da Nairar a farkon wannan wata na Oktoba, kuma sanarwar ta kara da cewa Nairar za ta fara aiki a ranar da aka kaddamar da ita.
Kaddamar da wannan Nairar ta intanet za ta sanya Najeriya a cikin sahun gaba na kasashen da suke da kudin yanar gizo a nahiyar Afrika, bayan da Ghana ta kaddamar da fara gwajin kudinta na eCedi a watan Satumba.
Manyan bankuna a fadin duniya na kokarin samar da makwafin kudadensu na intanet, biyo bayan habakar hada hada ta intanet da kuma yin gogayya da kudin Crypto da kasashe suka gaza sanya ido a kansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu