Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Malamai 3,795 mayakan boko haram suka kashe - Alkali

Shugaban Hukumar raya Jihohin dake Arewa maso Gabashin Najeriya Mohammed Alkali yace malaman makarantu 3,795 aka kashe a Jihohin Borno da Adamawa da Yobe, yayin da aka lalata makarantu sama da 1,500 sakamakon hare haren boko haram.

Iyayen daliban matan Chibok da mayakan boko haram suka kwashe
Iyayen daliban matan Chibok da mayakan boko haram suka kwashe © . AFP/Archivo
Talla

Alkali wanda ya gabatar da wadannan alkaluma lokacin da yake bude taron horar da malamai 300, yace ya zama wajibi hukumomi su mayar da hankali wajen sake gina makarantu da kuma horar da malaman da zasu koyar da dalibai a wannan yankin.

Shugaban kungiyar malamai a Najeriya Dr Nasir Idris yace a jihar Borno kawai malaman makarantu 800 aka kashe sakamakon wannan tashin hankali na kungiyar boko haram, abinda yayi matukar illa ga shirin karatun matasa.

Wannan yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya ya gamu da tashin hankalin mayakan boko haram na sama da shekaru 10, wadanda suka dinga kai munanan hare hare a makarantu suna kashe dalibai da malaman su.

Bayan kashe dalibai da malaman, mayakan kungiyar sun yi ta dibar wasu daga cikin su suna garkuwa da su, matakin da ya sanya iyaye da dama cire ‘yayan su daga makaranta.

Daga cikin munanan hare haren da ‘yayan kungiyar suka kai makarantu suka kuma kashe dalibai akwai kwalejin Buni Yadi dake Jihar Yobe inda suka kona dalibai da dama, yayin da kwashe dalibai mata daga makarantar Chibok ya gamu da mummunar suka daga sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.