Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Mutanen Sabon Birni na biyan haraji ga 'Yan bindiga - 'Dan Majalisa

‘Dan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto dake Najeriya wanda ke wakiltar Sabon Birni ta Kudu, Saidu Naino Ibrahim ya tabbatar da cewar har yanzu jama’ar da yake yiwa wakilci na biyan haraji ga ‘Yan bindigar da suka hana su zaman lafiya.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal © Twitter / @AWTambuwal
Talla

Yayin ganawa da manema labarai, Ibrahim yace akalla yankuna biyu ne kacal a mazabar sa da na abokin aikin sa dake Sabon Birni da basu biya kudin harajin da wadannan ‘Yan bindiga suka dora musu ba.

‘Dan Majalisar yace ya zama jiki a ga jama’ar wadannan yankin su biya kudi kafin zuwa gonakin su su noma da kuma lokacin da zasu girbe amfanin gonar da suka noma.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayan Dan Majalisar

 

01:02

NIGERIA-SAIDU NAINO IBRAHIM-1.07sec-2021-11-09

 

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust

Ibrahim yace ‘Yan bindigar da kan su suke zuwa akan babura, inda suke sanya musu abinda zasu biya, su kuma karba daga hannun su kafin basu damar gudanar da ayyukan su.

Wannan na daga cikin mummunar yanayin da mutanen Sabon Birni da kuma Sokoto ta Gabas suka samu kan su, sakamakon hare haren ‘Yan bindigar da suka hana zaman lafiya a sassan Jihar Sokoto da kuma Arewa maso Yammacin Najeriya.

Wadannan hare hare dai tuni suka tilastawa dubban mazauna Sabon Birni yin gudun hijira zuwa Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka, yayin da wasu da dama suka rasa rayukan su da kuma dukiyoyin su.

Yan gudun hijirar da rikici ya raba da muhallin su a Nijar
Yan gudun hijirar da rikici ya raba da muhallin su a Nijar © BOUREIMA HAMA/AFP

Hare haren ‘Yan bindigar dai ya fara ne daga satar shanu da sauran dabbobi, inda ya koma na mutanen da ake garkuwa da su domin karbar diyya da kuma satar abinci da dukiyar da suka tanada.

Lura da irin yadda wadannan matsaloli suka talauta mutanen yankin ya sa Yan bindigar suke sanyawa wasu daga cikin haraji kafin barin su su ziyarci gonakin su.

Rahotanni sun ce har wasika 'Yan bindigar kann aike ga kauyuka ko garuruwa domin a biya musu bukatar su ta karbar kudade ko kuma su kai hari garuruwan da zummar yiwa jama’a illa.

Sai dai kakakin rundunar 'Yan Sandan Jihar Sokoto Sanusi Abubakar yace babu gaskiya a labarin.

Jami'in yace sun gudanar da bincike dangane da zargi amma sun gano babu gaskiya a ciki, yayin da jami'an tsaron su ke can suna gudanar da aikin karkade Yan bindigar dake yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.