Isa ga babban shafi
NAJERIYA-SIYASA

Buhari ya taya Soludo murnar nasarar zaben Anambra

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murna ga zababben gwamnan jihar Anambra Charles Chukwuma Soludo wanda hukumar zabe tace shi ya lashe zaben da akayi a jihar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na taya zababben Gwamnan Anambra Charles Chukwuma Soludo murna
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na taya zababben Gwamnan Anambra Charles Chukwuma Soludo murna © Daily Trust
Talla

Sanarwar da shugaban ya gabatar ta hannun kakakin sa Garba Shehu ta bayyana aniyar Buhari ta aiki tare da zababben gwamnan wanda tuni yake cikin majalisar bada shawara ta tattalin arzikin Najeriya wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaro a Jihar Anambra da kuma kasa baki daya.

Shugaban ya yabawa hukumomin tsaro akan matakan da suka dauka wadanda suka taimaka wajen gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, yayin da ya jinjinawa Hukumar zabe saboda kammala zaben cikin nasara.

Baturiyar zaben jihar Farfesa Florence Obi ta bayyana cewar Farfesa Soludo ne ya lashe zaben saboda samun kuri’u 112,229 daga Jam’iyyar APGA, yayin da Valentine Ozigbo na PDP ya zo na biyu da kuri’u 53,807, sai kuma Andy Uba na APC da ya zo na 3 da kuri’u 53,807.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.