Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

'Yan bindiga sun kashe mutane 11 a sabon harin Batsari

Akalla mutane 11 aka tabbatar da mutuwar su, yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin da ‘Yan bindiga suka kai hari garin Batsari dake Jihar Katsinan Najeriya yammacin jiya, inda suka dinga bi gida-gida suna harbin mutane.

Gwaman Jihar Katsina Aminu Masari
Gwaman Jihar Katsina Aminu Masari © Dandago
Talla

Wannan al’amari na zuwa ne a daidai lokacin da aka katse hanyoyin sadarwa a yankin da kuma wasu sasan jihar Katsina domin baiwa jami’an tsaro damar kakkabe ‘Yan bindigar da suka addabi mutanen yankin.

Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa RFI Hausa da labarin harin da yadda ‘Yan bindigar suka dinga bi gida-gida suna harbe jama’a ba tare da samun dauki daga jami’an tsaro ba.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ‘Yan bindiga suka hana zaman lafiya a yankin arewa maso yammacin Najeriya, abinda ya kaiga asarar dimbin rayuka da dukiyoyi, yayin da wasu suka tsere suka bar garuruwan su domin tsira da rayukan su.

Gwamnatin jihar a karkashin Aminu Bello Masari tayi kokarin sasantawa da ‘Yan bindigar domin ganin sun aje makaman su amma abin yaci tura, inda wasu daga cikin su suka sake daukar makamai suka koma daji suna kai hari akan mutane ba tare da kaukautawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.