Isa ga babban shafi
Najeriya

Cikin Kwanaki Biyu 'Yan Bindigan Daji Sun Kashe Mutane 53 A Jihar Sokoto

Mutane akalla 57 ‘yan bindigan daji suka kashe a jihar Sokoto dake Najeriya cikin kwanaki biyu da suka gabata.

Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya Aminu Waziri Tambuwal. © Twitter / @AWTambuwal
Talla

Bayanai na nuna a karamar Hukumar Goronyo mutane  43 aka kashe Talata sai kuma mutane 14 a yankunan Sabon Birni dake Jihar ta Sokoto.

Harin na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci a kara tura sojoji yankin don su murkushe ‘yan bindigan daji da suka hana sukuni a yankin.

Wani mazaunin yankin wanda ya gaskata harin ya bayyana cewa ‘yan bindigan dajin sun mamaye kauyuka dake yankin Unguwar Lalle tun daren Talata inda suke ta ayyukan hashsha.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya fadi cewa suna ci gaba da kokarin kawo karshen hare-haren.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Kamaludeen Okunlola ya gaskata hare-haren da aka kai inda ya ce suna iyakacin kokarin kama ‘yan bindigan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.